Wasu ‘yan majalisar wakilai biyu na Amurka sun gabatar da kudurin dokar da zai ba baki wadanda basu da takardun zama kasa, da aka shigo da su kasar tun suna yara damar samun katin zama 'yan kasa.
‘Yar majalisa Lucille Roybal-Allard ta jam’iyyar Democrat da ‘yar majalisa Ileana Ros-Lehtinen ta jam’iyyar Republican ne suka gabatarda da kudurin wanda zai kare hakkokin irin wadannan bakin da ake kiransu DREAMers ta hanyar basu damar samun takardun zama ‘yan kasa.
Wannan kudurin ya samu ne a sakamakon namijin kokarin da wasu ‘yan majalisar biyu da suka hada da Dick Durbin na jam’iyyar Democrat da Lindsey Graham na jam’iyyar Republican suka yi a makon da ya gabata.
Ros-Lehtinen ta ce makasudin wannan kudurin shine don “kare na gari da kwararru a kasar mu kuma don inganata kasarmu,” ta kara da cewa manufar kudurin shine don a taimakawa mutanen da suka dade cikin fargaban za a maida su kasashensu na asali.
Facebook Forum