Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Kunar Bakin Wake Ya Tarwatsa Kansa A Kaduna


Dan Kunar Bakin Wake
Dan Kunar Bakin Wake

Ana cigaba da zaman zullumi a garin Keke na Millennium City dake Kaduna biyo bayan kunar bakin wake da wani mazaunin garin ya yi ta hanyar fasa bom a cikin gidan shi.

Cikin daren Lahadi zuwa safiyar jiya Litinin al'ummar garin Keke su ka wayi gari da wani tashin hankali sakamakon zagaye wani gida da jami'an tsaro su ka yi a kan hanyar Haske, daura da titin Lami bisa zargin mai-gidan na da hannu a harkar ta'addanci wanda bayan musayar wuta mutumin ya kashe kan sa.

Har zuwa ranar Talata hanyar zuwa gidan mutumin da ya kashe kan na shi na kewaye kuma akwai jami'an tsaro wadanda su ka ce ba za su iya tattaunawa da mu ba.

Wani Dan Kunar Bakin Wake Ya Tarwatsa Kansa A Kaduna
Wani Dan Kunar Bakin Wake Ya Tarwatsa Kansa A Kaduna

Maganar ta da bom dai ba sabuwar magana ba ce a Kaduna sai dai kuma wasu sun dauka ta zama tarihi.

Makwabtan wannan mutumin da ya kashe kanshi sun ce ba wanda ya san shi ko iyalin sa a yankin domin baya mu'amala da kowa.

Duk kokarin jin ta bakin jami'an tsaro da na gwamnati game da wannan batu ya ci tura sai dai sun tabbatar mana cewa za'a fitar da sanarwa kan wannan batu daga Abuja a yau Talata.

Saurari rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:26 0:00
XS
SM
MD
LG