Mutanen da harin da wani dan bindiga ya kai ya shafa sun kama daga shekaru biyar zuwa shekaru saba'in da biyu.
Shima maharin ya mutu kuma ba a san dalilin da ya sa ya kai wannan harin ba.
Masu bincike daga gwamnatin tarayya daga hukumar FBI, da kuma hukumar da ke sa ido akan harkokin taba sigari da barasa da bindigogi, sun hadu da jami’an tsaron yankin birnin Sutherland Springs, dake jihar Texas, mai nisan kilomita hamsin daga San Antonio.
Yau litinin Shugaban kasar Amurka Donald Trump, yace harin kan mai uwa da wabi, ba matsalar bindiga ba ce, amma matsalar tabin hankali ce wadda ta yi zafi.
Shugaba ya kara da ce wa lamarin da ya faru abin takaici ne. Bayan haka Shugaba Trump ya ce maharin ya na da matsalar tabin hankali.”
Shugaban na Amurka na sa ido akan wannan batun daga kasar Japan, kasa ta farko da ya je tsaya a ziyarar kasashe biyar da ya ke yi a nahiyar Asiya.
Facebook Forum