Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Cikin Kakin Soja Ya Bude Wuta Kan Sojojin Taron Dangi


Sojojin taron dangin kasa da kasa da ke girke a kasar Afghanistan
Sojojin taron dangin kasa da kasa da ke girke a kasar Afghanistan

Kungiyar kawancen tsaro ta NATO ce ta bayar da faruwar hakan a kudancin kasar Afghanistan

Kungiyar kawancen tsaro ta NATO ko OTAN, ta ce wani mutum cikin kakin sojojin kasar Afghanistan ya bude wuta kan sojojin taron dangi, ya kashe daya a cikin su.

A cikin sanarwar da NATO ta gabatar, ta ce sojojin taron dangin sun maida martani kan mutumin da ya bude mu su wuta a yau Lahadi a kudancin kasar Afghanistan.

Wannan harbi shi ne na baya-baya a cikin jerin munanan hare-haren da ‘yan bindiga sanye da kakin sojojin Afghanistan, ke kaiwa sojojin taron dangin kasa da kasa.

A wani tashin hankali na daban kuma, NATO ta ce sojin ta daya ya mutu a cikin fashewar bomb a yau Lahadi a gabashin kasar Afghanistan, daga nan ba ta yi wani bayani dalla-dalla ba game da harin.

A wani bangaren kasar kuma, an kashe wasu kwamandojin ‘yan Taliban biyu da ‘yan tawaye uku cikin fadan da aka fafata ranar Jumma’a da jami’an tsaro. A cikin wata sanarwar da ta gabatar, NATO ta ce daya daga cikin wadanda aka kashen, babban kwamandan ‘yan Taliban ne mai shirya hare-haren boma-boman gefen hanya da kuma tsara sauran hare-haren da ake kaiwa sojojin Afghanistan da na taron dangin kasa da kasa a duk fadin lardin Faryab.

Gudan kuma mataimakin kwamanda ne, kuma alkalin ‘yan Taliban wanda ya yi kokarin tilasta dokoki da hukuncin ‘yan Taliban akan fararen hular yankin.

XS
SM
MD
LG