Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Ba'amarike da Ya Bar Kungiyar ISIS Na Fuskantar Shari'a


Madridin mərkəzində çoban qoyun sürüsü otarır
Madridin mərkəzində çoban qoyun sürüsü otarır

Wani ba Amurke, wanda ya gudu daga kasar ya shiga kungiyar ISIS, kamin daga bisani yayi ikirarin ya sauya tunani yanzu ya dawo gida, inda zai fuskanci shari'a kan zargin ta'addanci.

Jiya Alhamis ne aka gurfanar da Mohammed Jamal Khwis, a gaban wata babbar kotun Amurka dake Alexandria Virginia. Gashi a yamutse sanye da wata bakar singileti. Mahaifinsa da mahaifiyarsa da dan uwansa suna daga-masa- hannu. Kamar yadda lauyansa yace, wannan shine karon farko da iyayensa suka ganshi tun bayanda ya shiga kungiyar ISIS.

Dan shekaru 26 da haifuwa, Jamal Khwis, ya shiga labarai ne lokacinda mayakan kurdawa da ake kira Peshmerge suka kama shi a arewacin Iraqi cikin watan Maris, inda ya zama kadan daga cikin mayakan kungiyar da aka kama a fagen yaki.

Ana tuhumar Mohammed Jamal da laifin taimakawa kungiyar ISIS. Idan aka same shi da laifi za'a yanke masa hukuncin daurin shekaru 20 a giudan yari da tarar dala dubu metan da hamsin.Kuma har karshen rayuwarsa hukuma zata ci gaba da sa ma rayuwarsa ido sosai.

XS
SM
MD
LG