Ana sauran 'yan mintuna kadan a fara zabensai wata wasika ta kunno kai dake dauke da sa hannun 'yan takara uku daga cikin wadanda zasu tsaya zaben.
A cikin wasikar suna zargin an tafka magudi sabili da haka sai suka fice daga wurin zaben. Wadan da suka ficen su ne Dr Muhammed Joga Suleiman, Alhaji M.B. Ibrahim Tumba da Barrister Yusuf N. Akirokuwen.
A martanin da ya mayar akan lamarin shugaban jam'iyyar APC din na jihar Taraba Alhaji Hassan Jika Ardo yayi fatali da zargin nasu. Yace maganrtasu bata da madogara ko kadan domin wadanda zasu zabi dan takara shugabannin ne daga gundumomi da shugabannin kananan hukumomi da na jiha. Wadannan su ne wakilai da zasu jefa kuri'a. Ba wasu mutane daban ba ne. Kana yace ba hakinsu bane su gudanar da zabe. An turo wasu daga uwar jam'iyyar su gudanar da zaben.
Jajiberen zaben Alhaji Ardo yace sai da suka yi taro da duk 'yan takarar. An zauna dasu. Wadanda zasu gudanar da zaben babu dan jihar Taraba cikinsu.
Hajiya Aisha Jummai Alhassan ita ce ta lashe zaben wanda ya sa ta zama mace ta farko da zata tsaya takarar kujerar gwamnan jihar Taraba. A firar da tayi da wakilin Muryar Amurka tace tayi farin ciki da nasarar da ta samu. Idan mutum na neman abu Allah kuma ya bayar to dole a yi masa godiya. Tace tana cikin matukar farin ciki.
'Yar takarar ta kira wadanda suka fice da su dawo su yi tafiya tare. Tace babu wani dan Taraba mai hankali da zai zabi PDP domin babu abun da jam'iyyar ta kawowa jihar Taraba sai masifa.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.