Yace maimako su kokarta suga cewa sun samar da yarjejeniyar da zata samar da gwamnatin hadin kan kasa.
A jiya alhamis ne Benardino Leon yake fadawa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a cikin jawabin sa na ban kwana cewa cikin yan makonnin nan da suka gabata ana samun tattaunawa mai muhimmamci game da wasu batutuwa da ada suke zama karan tsaye wajen samun hadin kan kasa daga sassan dake wa juna kallon hadarin kaji.
Yace sai dai kawai abinda har yanzu ba a samu ba shine wannan yarjeniyar a rubuce.
Amma ofishin na Majalisar Dinkin Duniya dake wannan kasar ta Libya yana nan yana ci gaba da kokarin ganin majiisar wakilai ta kasar ta Libya ita da majilisar dake cikin fadar kasar wato Libya sun gana domin cimma matsaya na sadidan wanda hakan zai bada damar cimma matsaya da kowa zai amince dashi game da makomar mulkin demokaradiyya.
Ita dai majilisar dake cikin birnin Tripoli da magoya bayan ta sune ke rike da babban birnin kasar tun shekarar data gabata, yayin da ta kori ainihin majilisar zartaswan da duniya ta amince da ita zuwa birnin Tabruk.
Dukkan su biyu dai sun dade suna budewa juna wuta wanda hakan yana daya daga ciki dalilan da ya haifar da kwararan yan gudun hijira zuwa kasashen Turai. Kana ya samar da yan kungiyar nan masu zazzafan raayi a cikin kasar ciki ko harda kungiyar nan ta ISIS.