Mawakan gargajiya da na zamani suka hada gwuiwar wallafa wakokin fadakar da kawunan jama'a a Jamhuriyar Niger da anfaninsu akan rayuwar yau da kullum.
Kula da yadda rigingimu suka addabi duniya ya sa mawakan shirya wakokin da zasu fadakar da jama'a. Mawakan na ganin akwai gudummawar da hadin gwuiwarsu zata bayar domin magance matsalar rigingimu.
Mawaki Mamman Sani Mati Adumulmula, ya bayyana dalilan shirya wakokin. Ya ce rikice rikice a Niger da Boko Haram ta haddasa har da kasashen Chadi, Kamaru, da uwa uba Nigeriya, da kuma rikicin dake aukuwa akan iyakar kasar da Mali suka sa mawakan shirya wakokin fadakar wa, musamman fadakar da matasa.
Wakokin na da zummar jawo hankulan matasa su bi hanyoyin da ba zasu jefasu cikin rigima ba ko jawowa kasar hutsuma ba. Ya kara da cewa babu wani ci gaba a ayyukan ta'addanci saboda ba addini ba ne ko kuma hanyar azurta dan'adam.
Rigingimun siyasa na cikin manyan matsalolin dake haifar da rarrabuwar kawunan jama'a a kasashe masu tasowa irin su Niger, dalili ke nan da mawakan ke kira a yi watsi da banbancen siyasa a duk lokacin da ake kokarin kare muradun kasa, inji fitacen mawaki Mummuni Yakuba Dankedanke. Ya ce siyasa ce ke sa mutum ya mance da kasarsa, ya ga gaskiya ya ce ba haka ba ne ko kuwa ya ga baki ya kirashi fari.
A tunanin mawakan, miyagun dabi'un matasa da sakacin mahukumta a mataki daban daban na cikin manyan dalilan dake janyo ambaliya cikin yawancin kasashen Sahel dalili ke nan da suka wallafa wata waka mai sun Harzuru wadda Yakuba Adamu, mai lakanin Yak D, ya ce tuni ta fara yin tasiri a kawunan jama'a.
Mawakan basu manta da matsalolin da 'yan cirani dake zuwa Turai ta barauniyar hanya suke fuskanta ba. Yak D, ya ce babu komi a Turai. Idan babu gidan kwana sanyi na iya kashe mutum. Baicin hakan bisa bashi ne mutane ke rayuwa a Turai. Yak D, ya ce ya gani da idanunsa ba gaya masa aka yi saboda ya sha zuwa.
Ga rahoton Souley Mummuni Barma da karin bayani
Facebook Forum