A jawabinsa na tsawon mintuna 15 da ya yi wa kasar, Shugaba Mahamadou Issoufou ya fayyace dalilan gwamnati na kebe babban kaso a tsarin kasasfin kudin kasar na 2018.
Ya yi hakan ne, a cewar shi, domin horas da jami'an tsaro tare da samar da bayanan sirri da kayan aiki na amfanin cikin gida da kuma wadanda suke taimakawa kasar ta fannin soji.
Kasashen yankin tafkin Chadi da suka hada da Najeriya da Chadi da Kamaru na da wata rundunar hadin gwiwa da ke yaki da kungiyar Boko Haram.
A wani gefen kuma kasar za ta taimaka wa sabuwar rundunar tsaro ta yankin Sahel mai kunshe da askarawan Mali, Burkina Faso da Mauritania wadda take da alhakin murkushe 'yan ta'addan arewacin Mali.
Ga rahoton Sule Barma da karin bayani.
Facebook Forum