Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wajibi Ne Gwamnatoci Su Dakile Zaman Kashe Wando


Wadanda ake zargin cewa ‘Yan Kungiyar Boko Haram ne
Wadanda ake zargin cewa ‘Yan Kungiyar Boko Haram ne

Kwamitin Majalisan Dattawan Najeriya da ta nada dangane da matasan da aka kasha a wani gida a Apo,Abuja ya gabatar da rahotonsa

Majalisar Dattawan Najeriya ta jaddada bukatar gwamnatocin kasar su gaggauta su kawo karshen zaman kashe wando da yawancin matasan kasar ke yi sanadiyar rashin abun yi lamarin da ya kai ga talauci da fatara da kuncin rayuwa har ma su haifar da baraza ga harkokin tsaro.

Wadannan na cikin shawarwarin da kwamitin bincike da ta nada kan kisan da aka yiwa matasa a Apo, Abuja da ta amince da su. Majalisar ta kafa kwamitin ne domin bincikar abun da ya kaiga kashe matasan a lokacin da jami'an tsaro suka kai samame. Kwamitin wanda Janaral Mohammed Magoro mai ritaya ya jagoranta ya jaddada bukatar gwamnatin tarayya ta kirkiro wasu sabbin dabaru wajen shawo kan tashin hankula a kasar.

Bayan majalisar ta kwashi sa'o'i tana muhawara kan rahoton wanda ya samu sa hannun sanatoci 20, Sanato Sahabi Yau daga jihar Zamfara wanda ya rasa wani daga mazabarsa ya ce nai gamsu da rahoton ba domin yawancin abun da aka ce kwamitin ya yi bai yi ba. Ya ce an nemi kwamitin ya binciko ko su matasan da aka kashe 'yan kungiyar Boko Haram.

Kamar ita majalisar dattawa majalisar wakilai tana nata binciken kamar yadda wani dan majalisar Ahmed Tukur Idris ya tabbatar. Ya ce kawo yanzu jami'an tsaro sun saki hudu daga cikin wadanda aka kama da yi masu kashedin kada su dawo cikin birnin Abuja har na tsawon shekaru uku.

Medina Dauda nada karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG