A cigaba da nuna damuwa kan makomar tsaro da kungiyoyi da daidaikun ‘yan Najeriya ke yi, kungiyar SERAP mai fafatukar kare ‘yancin dan adam da kuma tabbatar da rikon gaskiya da amana a gwamnati, ta nemi Shugaban Najeriya da Gwamnoninsa 36, su yi wa kasa bayanin abubuwan da su ke yi da kudaden da ake warewa domin inganta tsaro.
Kungiyar ta nemi bayanin kudaden tsaron, ciki har da wani bangare da aka fi sani da Security Vote ne, a wata takarda ta musamman da ta aike wa Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnonin nasa. Takardar wacce ke dauke da sa hannun Mataimakin Shugaban Kungiyar, Kolawale Oluwadare, ta ce Sashi na 14, karamin kashi na 2 na Kundin Tsarin Mulkin kasa na cewa tsaron rayukan al'ummar kasa da dukiyoyinsu sun tahalaka ne kacokan akan Gwamnati, kuma a yanzu haka al’umma na matukar fama da rshin tsaron.
SERAP ta ce dole ne a dauki matakin magance matsalar cikin sauri kafin lokacin da za a kafa sabuwar Gwamnati da ake shirin yi a kasar.
Wanan Mataki da SERAP ta dauka yayi daidai in ji tsohon mukaddashin shugaban kungiyar kwadago ta kasa Komred Isa Tijjani wanda ya yi bayani cewa dole ne Gwamnati ta fito fili ta bayyana wa 'yan kasar abinda ta ke yi da wadannan makudan kudade da ta ke warewa duk wata da sunan tsaro, wanda babu shi. Tijjani ya ce hakki ne na al'umma su san ko me ake yi da dukiyoyinsu.
To saidai Ministan Wasanni da Matasa, Barista Solomon Dalung ya ce batun Kudin Kulawa Da Tsaro (Security Vote) fa abu ne da Kundin Tsarin Mulki ya tanada, kuma babu wanda zai iya yin wani abu akai sai in an yi wa Kundin Kasar garambawul.
Shi kuwa wani mai rajin kare hakkin bil adama a Najeriya Yunusa Zakariya’u ya ce mafita ita ce a samu wata kafa da za a ba yan ‘kasa dama su fadi abinda suka ga ana yi da kudaden kasa kafin a kai ga wawure su. Ba wai sai gobara ta tashi har ta fara barna sannan a nemi kashe ta ba. SERAP dai ta ce za ta bi diddigin wanan takarda da ta rubuta har ta gano abinda ake yi da kudaden Security Votes a Najeriya.
Facebook Forum