Air Marshall Abubakar ya zanta da Muryar Amurka yayinda da ya kai ziyara Maiduguri inda ya bayyana manufar zuwansa.
Hafsan ya ce makasudin ziyarartasa shi ne samun daman ganawa da sojojinsa da suke Maiduguri kuma suna yaki da Boko Haram a duk fadin arewa maso gabas. Yace yana son ya tabbatar masu cewa suna tare dasu kuma sun yaba da aikin da suke yi wajen yakar 'yan Boko Haram.
Sojoji hamsin ne ya mannawa lambobin karin girma. Yace abun da ya yi kwamanada dinsu na iya yi amma ya zaba ya zo da kansa soboda ba sojojin tabbaci cewa ana sane dasu ana kuma jin dadin aikin da suke yi.
Yace sojojin sama suna yaki a sama da kasa. Akwai sojojin sama da suka marawa na kasa baya a fafatarwar da suka yi har ta kaiga kwato garuruwan da 'ayan Boko Haram suka mamaye da.
Sojojin saman burinsu ne su tabbatar cewa mutanen da aka rabasu da muhallanasu sun samu sun koma cikin kwanciyar hankali ba tare da tsangwama ba.
Hafsan yana da kwarin gwuiwar zasu shawo kan ta'adancin cikin wa'adin da shugaban kasa ba basu.
Ga karin bayani.