Uwargidan shugaban Amurka Barack Obama ta taimaka wajen yin fentin wani dakin jinyar masu cutar kamjamau yau Jumma’a yayinda ta kai ziyara kasar Botswana. Mrs Obama da kuma iyalinta dake tafiya tare da ita sun yi fentin wani sabon gini a cibiyar jinya ta Bostswana-Baylor dake Gaborone babban birnin kasar. Ana ginin dakin jinyar ne domin taimakawa kananan yara da matasan da ke dauke da kwayar cutar HIV/ ko cutar kan jamau. Daga nan mai dakin shugaban Amurkan ta halarci wani taron shugabanni mata inda ta sake jajada kiranta na tallafawa mata. Mai dakin shugaban Amurkant a bayyana cewa, iyayenta talakawa ne, amma bayanda ta je jami’a sai ta fahimci cewa, nasararta bata dogara kan asalinta ba, amma ta dogara ne kan irin kwazonta da kuma maida hankalinta ga abinda ta sa gaba. Mrs Obama zata kuma ziyarci shugaba Ian Khama kafin ta je kallon wani gandun daji da iyalanta. Kasar Botswana ce kasa ta biyu da ta yada zango a ziyarar kasashen Afrika biyu da ta kai kudancin Afrika da zumar karfafawa matasa manyan gobe guiwa dangane da batun shugabanci da kula da lafiyar al’umma.
Uwargidan shugaban Amurka Barack Obama ta taimaka wajen yin fentin wani dakin jinyar masu cutar kamjamau yau Jumma’a yayinda ta kai ziyara kasar Botswana.