Masar tace ta rage gibi a kasafin kudinta na badi, sabo da haka ba zata sa nemi tallafi daga hukumomin Kasa da kasa domin ta sami sukunin tafiyar da ayyukanta ba.
Tattalin arzikin Masar ya nosa lokacin zanga zangar da ta hambare gwamnatin shugaba Hosni Mubarak cikin watan febwairun bana,sakamon haka masu yawan bude ido suka dauke kafa, bugu da kari ma’aikatan kasar suka fada yaje yajen aiki da nufin neman karin albashi,wadda ya kara kassara kasuwanci.
Da farko jami’an Masar sun bukaci kamar dala milyan dubu shida da milyan metan daga Bankin Duniya da asusun bada lamuni IMF, domin tallafawa aikace aikacen gwmanati a kasafin kudin kasar na badi, da zai fara aiki daya ga watan gobe.
Amma ministan kudi Samir Radwan, ya fada Asabar cewa gwamnatin ta sake nazarin kasafin kudinta ta rage gibin, har ma bata bukatar tallafi daga bankin Duniya.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ambaci ministan yan acewa masar ta rage kasafin kudinta daga dala milyan dubu 86 zuwa dala milyan dubu 82. Kasafin kudin da farko yayi hasashen gibi na dala milyan dubu ashirin da takwas, adadin da yanzu ya ragu da kamar dala milyan dubu shida.