Jiya Laraba ce aka yi bikin rantsar da sabbin wakilai da tsoffi na majalisar dokokin Amurka,a majalisar wakilai Jam’iyyar Republican ce take da rinjaye.
An zabi dan Republican John Boehner kakakin majalisar wakilai,a jawabinsa ya gayawa majalisar cewa Amutrka tana fuskantar manyan kalubale,inda ko wani mutum daya cikin 10 bashi da aikin yi,a yayinda kudin kiwon lafiya yake kara hau-hawa ga jama’a da kamfanoni. Yace masu zabe sun aika da sako a bayyane cewa basa jin dadin yadda al’amura suka kasance cikin kasan nan.
’Yan Republican sun sami galaba ta ko wani sashen a fadin Amurka azaben da aka yi cikin watan Nuwamba,wanda ya janyo raba gwamnati dake hanun jam’iyu biyu.
Kakakin fadar White House,Robert Gibbs yab fada jiya laraba cewa gwamnatin Mr. Obama tana sha’awar ganin ana ci gaba aiki da irin hada kai da aka samu bayan kammala zabe,kamin majalisar dokoki ta tafi hutun karshen shekara.A lokacin ne wakilan majalisar dokokin suka zartas da dokoki kan rangwamen haraji,soke dokar hana ‘yan luwadi aikin soja,da kuma amincewa da yarjejeniyar rage makaman nukiliya tsakanin Amurka da Rasha.
Haka kuma ‘yan Republican wadanda suka sami Karin wakilai kodashijke har yanzu sune basu da rinjaye sunce zasu yi yunkurin rusa dokar garambawul din kiwon lafiya da shugaba Obama ya yi.