Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton tana kan hanyarta zuwa yankin tekun pasha da zumar nemarwa sabuwar gwamnatin Iraq goyon baya

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton (file photo)

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton tana kan hanyarta zuwa yankin tekun pasha da zumar nemarwa sabuwar gwamnatin Iraq goyon baya, da kuma daukar mataki mai tsanani kan Iran sabili da ayyukanta na nukiliya. Sakatariya Clinton wadda ta tashi daga Washington jiya da yamma, zata yada zango a Oman da kuma Qatar dake daular larabawa. Jami’an ma’aikatar harkokin wajen Amurka sun ce zata yiwa shugabannin yankin tekun pasha bayani kan burin Amurka a tattaunawa ta gaba da za a yi da Iran makon gobe a Istanbul. Suka ce, babbar jami’ar diplomasiyar zata kuma tattaunawa kan hanyoyin tallafawa yankin game da aiwatar da takunkuman da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa Iran. Dangane kuma da Iraq, jami’an ma’aikatar harkokin wajen Amurkan suka ce, Washington zata yi kira ga kasashe a yankin su bude ofisoshin jakadanci a Bagadaza.

XS
SM
MD
LG