Jihar Borno ita kadai ce jihar da ke makwabtaka da kasashen Afirka guda uku da suka hada da Chadi, da Nijar da kuma Kamaru. Baya ga matsalar rikicin Boko Haram, jihar na fuskantar sauran matsaloli musamman na fasa kwori da ya shafi dukkan makwabtan kasashen uku.
Kwanturolan da ke kula da jihohin Borno da Yobe, Mista Angbalaga Joshua ya bayyana cewa an rufe iyakoki guda 10 cikin guda 13 da ake da su a jihohin biyu sakamakon matsalar tabarbarewar tsaro. A yanzu haka suna gudanar da kwarya-kwaryar ayyuka ne akan iyakokin da suke Gamboru, da Banki da kuma Geidam.
A ranar 29 ga watan Yuni ne ya ce suka kama wata babbar mota dauke da shinkafar waje da kuma wake - wanda aka yi amfani da shi domin batar da sawu.
Kwanturolan ya yabi rundunar sojin Najeriya da ya ce da taimakonsu ne aka samu nasarar kame wadannan kayayyakin.
Kwanturolan Jihar Borno yayi karin haske game da ayyukansu a wannan yankin, inda ya bayyana abubuwan da ba a haramta shigowa da su ba: kifi,wake, masara da kuma dabbobi kamar shanu, awaki, tumaki da sauransu, wadanda kawai suke karban kudin fito akansu.
Sannan ya ce akwai umarnin da aka ba su na cewa duk abinda ya shafi abinci, ko daga ina ne idan kwastam ta kama, to a yi saurin kai wa 'yan gudun hijira.
Baya ga matsalar tsaro, kalubalen da suke fuskanta shine yadda hanyoyi basa biyuwa musamman a lokacin damina.
Saurari rohoton
Facebook Forum