Tun lokacin da Malam Bazoum Muhammad ya canji shugaban kasar Nijar Issoufou Muhammadou a matsayin shugaban PNDS mai mulki, sai wannan lokacin ne ya fita rangadin ganawa da magoya bayansa a cikin jihar Maradi.
A jawabinsa ya godewa Allah da jama'a da suka goyi bayansa kana ya yiwa masu adawa dashi da jam'iyyar shagube. Yana cewa shi ya bi hanyar gaskiya ce kodayake tana da tsawo amma ta kaiga nasara. Yace banbancinsu da 'yan adawa shi ne jagoranci nagari da Issoufou Muhammadou ya yiwa jam'iyya yake kuma yiwa kasar. Yace shugaban kasa ba dan kasuwa ba ne. Yace 'yan Nijar sun yadda dashi. Ya bada tabbacin cewa yadda shugaba Issoufou ya tanadawa jam'iyyarsa haka zai tanadawa kasar Nijar.
Wani jigo a jam'iyyar PNDS Malam Kallahu ya tofa albarkacin bakinsa. Yace ana biki koina na goyon baya da na godiya saboda aikin da gwamnatin PNDS da Issoufou Muhammadou suke yi da zuciya guda.Ya gargadi jama'a da siu cigaba da kawowa jam'iyyar mutane bisa ga ayyukan alherin da take yi.
Mata ma ba'a barsu baya ba. Shugabansu ta fito ta roki mata su fito lokacin zabe su zabi jam'iyyar domin a samu cigaba.
Ga rahoton Chaibou Mani.