A yau Litinin Ministan cikin gidan Tunisia ya fada cewa dakarun kasar sun kashe mayakan sa kai 21, wadanda suka kai hari a wani ofishin ‘yan sanda da wani sansanin sojin kasar da ke kusa da kan iyakar kasar Libya.
Jami’an sun ce an kashe akalla fararen hula hudu da wani soja guda a arangamar da aka yi a garin Ben Guerdane dake kudu maso gabashin kasar.
Bayan arangamar, hukumomi sun umurci mazauna yankin da su zauna a cikin gidajensu.
Dakarun kasashen yammacin duniya dai na taimakawa takwaroinsu na Tunisia, yayin da ake kara nuna damuwa, kan yadda mayakan sa-kai, ciki har da na kungiyar IS ke tsallaka kan iyaka domin kai hare-hare.
A makon da ya gabata, Burtaniya ta bayyana cewa za ta aika da dakarunta 20 da za su taimaka wajen kare kan iyakar.