Kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar Borno Victor Isoko, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin yace wani dan Civilian JTF da wata mace daya da ‘ya’yanta biyu ne suka rasa rayukansu sakamakon tashin wadannan boma boman, yayinda mutanen da suka samu raunuka an kai su asibiti domin yi masu magani.
DSP Isoko, yace na miji daya da ‘yan mata biyu ne suka kaddamar da harin sai dai bai bada adadin shekarunsu ko kuma ta inda suka shiga garin ba.
Rahotanin daga kauyen na cewa wannan shine karo na uku cikin wata daya da ‘yan kunar bakin wake ke kai kauyen hari duk da yake akwai jami’an tsaro kewaye da kauyen amma wanna shine karon farko da suka sami nasarar kashe mutane har hudu.
‘Yan kwanakin nan dai ana ta ci gaba da samun hare haren ‘yan kunar bakin wake da kuma kai hare hare kan jama’a, ko a kwanakin baya wasu mahara sun kai hari kan jami’an Soja dake garin Magumeri inda suka hallaka jami’an Soja.
Facebook Forum