A jiya ne ‘yan kasar Faransa suka kada kuri’a a zaben kananan hukumomin kasar, duk da cewa ana ta hasashen jama’a ba zasu fito ba saboda barkewar cutar Coronavirus da tsoran cudanya da jama’a.
Shugaba Emmanuel Macron ya nace cewa za a samu koma baya a demokradiyyar kasar idan ba a gudanar da zaben a kan lokaci ba.
Dubban magadan gari da shugabannin kananan hukumomi ne za a zaba a wannan zabe mai zagaye na biyu.
A kokarin kasar ta Faransa na yakar cutar Coronavirus ta rufe hasumiyar Eiffel Tower da kuma shiyyar Louvre.
A jiya Lahadi ta rurrufe gidajen cin abinci da wuraren kallo da kantuna, wadanda ba su zama tilas ba a fadin kasar.
Za a gudanar da zagaye na biyu na zaben ran 22 ga watan Maris.
Facebook Forum