Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon shugaban Sojojin Sudan ta Kudu Ya Kafa Sabuwar Kungiyar 'Yan Tawaye


Wasu 'yan gudun hijira daga Sudan ta Kudu da yakin basasa ya daidaita
Wasu 'yan gudun hijira daga Sudan ta Kudu da yakin basasa ya daidaita

A Sudan ta Kudu wani tsohon shugaban hafsan hafsoshin kasar Janar Paul Malong Awan ya kafa sabuwar kungiyar 'yan tawaye da shan alwashin cewa zai tabbatar da kafa dimokradiya a kasar

Tsohon shugaban sojin Sudan ta Kudu Janar Paul Malong Awan kuma shugaban rundunar da ake kira Sudan People’s Liberation Army (SPLA) a takaice, ya kafa wata sabuwar kungiyar yan tawaye mai suna South Sudan United Front (SSUF) a takaice.


A cikin wata sanarwa jiya, Janar Awan ya bayyana manufofin sabuwar kungiyarsa, wanda yace zata yaki cin hanci da rashawa, ta kawo karshen kashe kashe, kana ta kuma dora Sudan ta Kudu a kan tafarkin demokaradiya da adalci da samar da daidaito da walwala.


Awan ya kuma yi alkawarin mutunuta yarjejeniyar tsagaita wuta da bangarori masu yaki da junada aka sanya hannu a cikin watan Disemban bara. Ya kuma yi kira ga kungiyar raya tattalin arzikin kasashe dake yankin da ake kira IGAD a takaice ta kyale sabuwar kungiyarsa ta shiga sahun tattaunawar da za a yi a ranar 26 ga watan Afrilu a birnin Addis Ababa na Habasha.


Mai Magana da yawun kungiyar ta South Sudan United Front, Sunday De John ya fadawa shirin Muryar Amurka; "South Sudan in Focus" a jiya Litinin daga birnin Nairobi na kasar Kenya cewa, sabuwar kungiyar zata yi aiki domin samar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG