Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Somalia Ta Kwace Wasu Makudan Kudi A Filin Jiragen Sama Dake Mogadishu


Filin jiragen sama na Mogadishu inda aka kano dalar Amurka kusan miliyan goma da aka shigo dasu daga hadaddiyar Daular Larabawa ko UAE
Filin jiragen sama na Mogadishu inda aka kano dalar Amurka kusan miliyan goma da aka shigo dasu daga hadaddiyar Daular Larabawa ko UAE

Hukmomin Somalia sun musanta iikirarin da Jakadan Daular Larabawa yayi na cewa kudin da aka kwace a filin jiragen sama dake Mogadishu na albashin sojojin Somalin ne

Jami’an tsaron Somalia sun ce sun kwace wasu makudan kudade a filin saukar jirage sama a Mogadishu daga birnin Abu Dhabi na kasar, Hadaddiyar Daular kasashen Larabawa, ko kum UAE atakaice.


Wasu manyan jami’an tsaro biyu sun shaidawa sashen Somaliyanci na Muryar Amurka cewa, an ajiye jakkuna uku da suke dauke da dala miliyon tara a babban bankin Somalia , ana gudanar da bincike a kansu.

Jakadan Daular kasashen Larabawan Mohammed Ahmed Othman Al-hammad, ya fadawa sashen Somalianci cewa, kudin ba na ofishin jakadanci ba ne. Yace kudi ne na ma’aikatar tsaron Somlia kuma zasu biya sojojin kasar albashin su.


Yace gwamnati na sane da zuwan wadannan kudade da za a baiwa sojoji tun kafin su zo. UAE tana horar da sojojin Somalia a Mogadishu da kuma kimanin yan sandan tsaron gabar teku dubu daya a yankin Putland


Jami’an Somalia sun hakikance cewa kudin ba na sojojin kasar ba ne. Albashin sojojin bai kai dala milyan daya ba, kuma wannan kuma sun kusan dala milyan 10, inji wani jami’i.


Dangantaka tsakanin Somalia da UAE tayi tsami tun shekarar da ta gabata, lokacin da gwamnatin Mohammed Abdullahi Mohammed ta ki amincewa da yanke hulda da Qatar kuma ta dauki matsayin ba ruwanmu a kan takaddama tsakanin Saudiya da Qatar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG