Tsohon shugaban Najeriya karkashin mulkin Soja Janar Ibrahim Babamasi Babangida ya yi tsokaci kan cire tallafin man fetir da gwamnatin tarayya ta yi.
A cikin wata hira ta musamman da Muryar Amurka Janar Babangida ya bayyana cewa, kamata ya yi gwamnatin tarayya ta ci gaba da tattaunawa da kungiyoyi da kuma wayar da kan jama'a kan muhimmancin janye tallafin man fetir har zuwa karshen kwatar farko ta wannan shekarar kamar yadda ta bayyana niyar yi tun farko.
Janar Babangida yace janye tallafin man fetir din a wannan lokacin bai yi daidai ba ganin irin halin da kasar ke ciki tare da kalubalar tsaro da ake fuskanta da suka hada da hare haren boma bomai da aka kai na baya bayan nan da kuma dokar ta baci da gwamnatin tarayya ta kafa a kananan hukumomi goma sha biyar na kasar.
Saurari cikakkiyar hirar a sama.
Saurari