Kwana daya bayan da aka cire talafin mai a Nigeria, farashin mai yayi tashin gwaron zafi har fiye da ninki daya.
An sayar da mai daga kimamin centi arba'in zuwa centi tamanin da takwas kowane lita guda litinin din nan.
Shedun gani da ido su bada rahoton cewa sai da yan sanda suka yi amfani da barkonon tsohuwa a Abuja domin tarwatsa mutane da suka taru domin nuna rashin amincewarsu ga tsadar mai.
Kungiyar kwadagon Nigeria da ake cewa NLC a takaice da kuma kungiyar harkokin kasuwanci sunce cikin yan kwanaki masu zuwa zasu bukaci ayi zanga zangar nuna rashin amincewa a duk fadi kasar. Kungiyoyin sun fada a wata sanarwar hadin gwiwar da suka gabatar cewa cire tallafin mai ya nuna cewa ba'a tausayin talaka.
Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan yace maimakon a kashe kimamin dala biliyan bakwai da rabi wajen tallafin mai gara ayi amfani da kudin wajen inganta harkokin kyautata jin dadin jama'a.
A duk rana Nigeria kan hako fiye da garwa miliyan biyu na danyen mai. To amma ala tilas take sayo man da aka tace daga wasu kasashe domin madatsun man kasar basu da ingantattun hanyoyin tace ko kuma sarafa mai.