Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Kakakin Rundunar Sojojin Saman Najeriya Ya Rasu


Air Commodore Wap Maigida
Air Commodore Wap Maigida

Air Commodore Wap Maigida ya rasu ne a gidansa haka bakatatan a daren ranar Lahadi inda rahotanni suka ce yanke jiki ya yi ya fadi.

Babban sojan saman wanda a ranar 6 ga watan Janairu wannan shekara ta 2023 ya zama mai magana da yawun rundunar sojojin saman kasar bayan da ya canji Air Commodore Edward Gabkwet.

Maigida da a baya ke rike da matsayin Kwamandan sojojin sama a jihar Filato, ya kuma yi babban dogarin Babban Hafsan Hafsoshin mayakan saman kasar wato ADC a zamanin Air Marshal Jonah Wuyep.

Tuni dai shedkwatar sojojin saman Najeriya ta bayyana rasuwar jami’in nata a matsayin wani abu mai tada hankali.

Air Commodore Maigida, wanda dan asalin jihar Filato ne da ke arewa ta tsakiyar Najeriya, kuma dan kwas na 42 ne na makarantar Hafsoshin sojojin kasar wato NDA da ya fara aikin soji a shekarar 1995.

Marigayin wanda yak e da digiri na biyu ka harkokin dabarun tsaro, ya yi kwasa-kwasai a cikin da wajen Najeriya kamar kasashen Sweed, Indenosia da Burtaniya.

Ya kuma taba rike mukaddashin Daraktan Sadarwa a Shedkwatar Tsaron Najeriya.

XS
SM
MD
LG