Jirgin wanda ya tashi da nufin zuwa Minna a jihar Neja ya juyo bayan da injinsa ya samu tangarda wanda kuma ya samu hadarin lokacin da yake kokarin sauka.
Sai dai dukkannin mutune bakwai da ke cikin jirgin sun mutu nan take.
A cikin wata takaitacciyar sanarwa da ya aikewa VOA, kakakin rundunar sojan saman Najeriya, Air Vice Marshall Ibikunle Daramola, ya ce jirgin mai suna NAF BEECHCRAFT KingAir B350i ya samu hadarin ne sakamakon tangardar inji, yayin da yake sauka a filin jirgin saman Abuja.
Wani da ya shaida aukuwar hadarin ya ce jirgin ya yi ta tangal tangal a lokacin da yake yin kasa kafin daga bisani ya fado kan wata bishiyar mangwaro kusa da wani rafi da ke kauyan Basa.
Tuni dai babban hafsan hafsoshin sojojin saman Najeriya, Air vice marshal Isiyaka Amao, ya bada umarnin kaddamar da bincike don gano musabbabin aukuwar hadarin.