WASHINGTON, DC —
Yayin da guguwar iskar canza sheka ke cigaba da kadawa musamman a arewacin Najeriya da alamu tsohon gwamnan jihar Zamfara ya fi karfin guguwar.
A ganawarsa da manema labaru a Abuja tsohon gwamnan jihar Zamfara Mahmud Aliyu Shinkafi ya musanta jita-jitar da wata jarida ta yayata cewa ya bar PDP. Ya ce sam bai bar jam'iyyar PDP ba. Ya ce sauya jam'iyya yanzu ba dabara ba ce. Ya ce jaridar daga Sokoto a ke bugata. Ta yi karya sau daya ta yi na biyu yanzu kuma ga na uku ta yi. Ya ce zamansa a PDP ya damu wasu mutane amma sun manta cewa Ubangiji ke bada mulki. Ya ce su da suka karbi mulki ai shi da magoya bayansa basu ce komi ba domin sun san Allah ke bayarwa. Ya ce yanzu zasu yi takara PDP ta sake kama Zamfara lamarin dake tayar masu da hankali ke nan. Ya ce zasu yiwa PDP aiki cikin ruwan sanyi har Allah ya dawo masu da mulki a jihar Zamfara. Ya ce PDP zata dawo a samu zaman lafiya da cigaba a jihar da yaddar Allah.
Ya ce an sha bugo masa waya ana tambaya maganar gaskiya ce yana cewa ba gaskiya ba ce. Ya ce domin wasu mutanen waya bata kaiwa wurinsu amma ana jin Muryar Amurka koina shi ya sa ya nemi ya fadawa kowa ta kafar Muryar Amurka kowa ya ji. Ya ce jihar Zamfara kashi tamanin PDP ne kuma idan Allah Ya yadda kafin zabe za'a samu kashi casa'in ko fiye da haka.Duk wata bakar dabara da zasu bi mutanen Zamfara sun san da ita. Karya da yin anfani da addini a yaudari mutane sun kare.
Tsohon dan majalisar wakilai daga Zamfara Sani Anka ya ce zasu dawo da taken nan da suke yiwa Shinkafin na ta zarce. Ya ce lokaci suke jira domin Mahmud Shinkafi ya shimfidawa mutanen Zamfara alheri. Yanzu mutanen Zamfara sun gane kuskuren da suka yi. Idan zabe za'a yi na tsakani da Allah Mahmud zai ci zabe ko yau aka yi shi.