Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Meyasa Shugaban Majalisar Dokokin Kano Yayi Murabus?


Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso
Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso

Talatannan ne, Alhaji Gambo Sallau wanda shine shugaban majalisar dokoki ta jihar Kano na goma, tun kafuwarta a shekara ta 1979, ya sanar da saukarsa daga kujerar shugabancin majalisar.

Ko da yake, shugaban yayi tattaki zuwa birnin tarayya Abuja tun cikin karshen makon jiya. Wakilin Muryar Amurka Mahmoud Ibrahim Kwari yayi magana da shi domin tabbatar da matakin da ya dauka, na barin shugabancin majalisar.

Alhaji Gambo yace “a yau Talata, hudu ga watan biyu, shekara ta 2014, ni Gambo Sallau, shugaban majalisar dokoki ta jihar Kano, na sauka daga wannan mukamin, saboda dalilai na siyasa. Ba zan iya komawa wata jam’iyya daga jam’iyyata, ta PDP ba.”

“Ina so in yi amfani da wannan dama, in yi wa Allah (S.W.T) godiya, saboda dama da Ya bani, don in jagoranci majalisar dokokin jihar Kano na shekara biyu da wata biyu. Allah Ya bani dama na jagorance ta cikin nasara. Ina yiwa abokan aiki na, na majalisar dokokin jihar Kano godiya, saboda hadin kai da goyon baya da suka bani a lokacin da nake jagorantar su.” A cewar tsohon shugaban.

Tuni dai wakilan majalisar suka zabi mataimakinsa Honorable Isiyaku Ali Danja, a matsayin sabon shugaban majalisar, yayinda aka zabi tsohon shugaban masu rinjaye Honorable Hamisu Ibrahim a matsayin maimakin shugaba.

Litininnan da ta wuce ne wakilai 27 na jam’iyyar PDP a zauren majalisar sukayi sauyin sheka zuwa jam’iyyar APC lamarin da saka adadin ‘ya’yan APC a zauren majalisar ya kai 34 yayinda PDP ke da 6.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG