Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben June 12, 1993 da aka soke Alhaji Bashir Tofa ya rasu.
Rahotanni na nuni da cewa Tofa ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya yana da shekara 74.
Mariyagin ya tsaya takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar NRC inda ya kara da dan takarar SDP MKO Abiola.
Abiola ya lashe zaben, amma gwamnatin mulkin soji karkashin Janar Ibrahim Babangida ta soke zaben.
‘Yan Najeriya da dama sun yi ittikafakin cewa zaben shi ne mafi sahihanci da Najeriya ta taba yi.
Tofa na daya daga cikin dattawan Arewacin Najeriya da kan fito fili su yi tsokaci kan yadda za a samar da maslaha game da matsalolin Najeriya, musamman a arewacin kasar.