A hirar ta da Muryar Amurka, mahaifiyar Hanifa ta ce sun yi ta fadi tashi suna neman bayanai da za su kai ga gano Hanifa, amma hakar su bata cimma ruwa ba, kuma ba wanda ya tuntube su domin neman kudin fansa kamar yadda masu garkuwa da mutane su ka saba yi, sai bayan kwanaki 38.
Mahaifiyar Hanifa ta bayyana cewa, a rana ta talatin da takwas da bacewar Hanifa, mahaifin Hanifa ya ga takarda a kofar gida wanda ya kasance karon farko da Abdulmalik Tanko, malamin makarantar da ya yi garkuwa ya kuma kashe Hanifa ya fara tuntubar iyayenta. Ta ce bayan nan sai aka fara aika mata da sakonni ta wayar salula da Fulatanci cewa “mu muka dauki Hanifa” sai dai bayan wannan sakon ba ta sake ji daga wanda ya yi garkuwa da Hanifa ba, sai bayan da hira da wata kafar watsa labarai inda suka bayyana cewa, basu da hujjar tabbatar da cewar an yi garkuwa da ‘yarsu.
Mahaifiyar Hanifa ta ce ranar da suka yi wannan hirar, Abdulmalik Tanko, ya sake aika mata sako da Fulatanci cewa, “kun ce ba mu baku hujja ba, to zamu aiko maku da rigar sanyin Hanifa, da bajen makarantar ta, da hotonta, ta yiwu ku yarda.”
Tabbacin Garkuwa da Hanifa
Bisa ga bayanin mahaifiyar Hanifa,
“Ranar da Hanifa ta kwana talatin da tara, na fito kofar gida, na ji mai kwashe shara, na bashi shara, na tura kofa kawai sai na ga wata bakar leda a daure, sai na ce wa mai shara, menene wannan ka yar min? Sai ya ce “a’a, a wurin na ganshi”, Sai na ce, to bude min, kawai sai ya yaga ledar. Lokacin da ya yaga ledar, “I was shocked” (na gigice), saboda Suwaitar (rigar sanyin) Hanifa na gani, so (saboda haka) sai na dauko na shiga gida. Da na shiga gida kawai sai na bude. Gida na biyu ne. sai na tafi daya gidan inda maigida ya ke, sai na je na buga, na ce, na gaya maka, garkuwa da Hanifa aka yi. Menene hujja, na ce gata!. Nace wanda ya ke aika min da sako ta wayar hannu shi ya dauki Hanifa. Menene ya sa, sai na bude mashi, na ce ga shi!. Ina bude rigar suwaitar, sai bajen Hanifa ya fado, sai hoton Hanifa. Amma hoton da aka dauke ta, sai aka je aka sa shi a computa. Aka sake daukar hoton, sabili da haka bata fita sosai ba, amma Hanifa ce.”
Yadda Wasu Mutane Suka Kashe Dan Makwabcinsu Bayan Sun Karbi Miliyan Biyar Kudin Fansa
GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali, Waiwaya Maganin Mantuwa: Kashi Na Daya, Disamba 06, 2018
Murja Suleiman, mahaifiyar Hanifa ta bayyana cewa, tun daga ranar ta fita a hayyacinta. Ta ce bata sake barci ba. Bata sake cin abinci ba. Bata kuma gayawa kowa ba.
A nashi bayanin, mahaifin Hanifa, Abdulsalam Abubakar ya bayyana cewa, malamin na daya daga cikin wadanda suka fara zuwa su yi masu jaje lokacin da suka tabbatar da bacewar Hanifa. Bisa ga cewarshi, dama Hanifa tana zuwa wata makarantar Islamiya ne kafin suka tsaida shawarar cire ta daga makarantar su ka maida ita makarantar da ake kira “Noble Kids” domin ta fi kusa da gida. Yace duka- duka Hanifa ba ta shekara a makarantar ba wannan abin takaicin ya faru.
Tuni aka kama malamin makarantar Abdulsalam Abubakar wanda magidanci ne da ke da kananan yara uku, da kuma sauran mutane biyu da ake kyautata zaton suna da hannu a lamarin da suka hada da wata mace.
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin rufe makarantar da Hanifa ta ke zuwa kafin gamuwa da ajalinta, inda kuma malamin ya binne ta kafin hukuma ta tono gawarta.
Kasa da mako guda bayan kama malamin da kuma tono gawar Hanifa, matasa suka huce fushin kisan Hanifa ta wajen cinnawa makarantar wuta, duk da yake hayar ginin mai makarantar, Abdulsalam Abubakar ya ke yi.
Garkuwa da kisan Hanifa dai ya dauke hankalin al’umma a ciki da wajen Najeriya, inda da dama suka bukaci gwamnati ta yanke wa malamin hukumcin.
Gwamnatin Najeriya ta ayyana masu garkuwa da al’umma a matsayin ‘yan ta’adda, yayinda matsalar garkuwa da al’umma ke kara ta’azzara, lamarin da ya kara nawaitawa al’umma biyo bayan matsalar tsaro da ake fama da ita a kasar shekara da shekaru, sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram.
Wannan dai ba shi ne karon farko da aka yi garkuwa, aka kuma kashe karamin yaro a jihar Kano ba. A shekara ta dubu biyu da goma sha tara, wata mace mai suna Fadila Mohd Surajo, ta sace ‘yar kawarta ‘yar shekaru takwas mai suna Aisha Sani, a Tudun-Wada, Karamar Hukumar Nassarawa, ta jefa ta a rijiya bayan rufe ta a ban daki na tsawo kwanaki sabili da iyayan yarinyar sun gaza biyan kudin fansa Naira miliyan goma da ta nema a cikin kan lokaci.
Ko a watan Yunin shekarar da ta gabata, an kama wani mutum mai suna Auwalu Abdulrashid a Karamar Hukumar Tofa wanda ya amsa laifin kashe wata yarinya ‘yar shekara 13, bayan iyayenta sun nemi rangwami daga naira miliyan daya da ya nema suka amince zasu biya Naira dubu 400 domin a sako ‘yarsu mai suna Zuwaira. Auwalu ya amsa cewa, ya tafi da Zuwaira wani gini da ba a kamala ba, inda ya makare ta, daga baya ya dauki wuka ya yanka makogwaronta. Ya kuma ce kafin garkuwa da Zuwaira, ya yi garkuwa da kanenta dan shekaru uku ya nemi a biya kudin fansa Naira miliyan biyu, aka kuma bashi Naira dubu 100 kafin ya sako shi.