Wani rahoton cibiyar Open Budget Survery ya gano cewa har yanzu ana fama da rashin haske a game da yadda ake aiwatar da kasafin kudaden shekara shekara a kasashe da dama na nahiyar Afrika bayan gudanar da bincike a kasashe 117 na duniya akan kasafin shekarar 2019.
Lamarin da ya sa kungiyoyin ci gaban jama’a a Jamhuriyar Nijar shirya wata mahawara domin nazarin dalilan dake haddasa wannan matsala.
Rashin baiwa ‘yan kasa damar shiga al’amura a lokacin aiwatar da kasafin kudade da rufe masu hanyoyin zuba ido don tantance irin wainar da ake toyawa da kudaden kasa na daga cikin muhimman sharudan da cibiyar Open budget Survery ke maida hankali akansu wajen tantance kokarin gwamnatocin duniya akan maganar haske da adalcin aiwatar da kasafin kudade.
Rahoton na shekarar 2019 ya gano wasu kasashen Afrika da suka yi rawar gani amma ya ayyana kasashen Sahel a sahun wadanda ke da karancin matakan samarda haske akan maganar aiwatar da kasafin kudadensu inji jagoran mahawarar da kungiyar AEC ta shirya Malan Abba Hassan.
“Idan ana neman kudaden da za a aiwatar da wasu ayyuka a kasa, al’umma ke biya, to bai kamata ace basu da labarin yadda ake kasha wadannan kudadden ba.”
Shekaru sama da 10 kenan cibiyar Open Budget Survery da wasu kungiyoyin kasashen yammaci ciki har da na kasar Amurka ke gudanar da irin wannan bincike na hadin gwiwa da kungiyoyin ci gaban al’umomin Afirka domin ankarar da gwamnatoci muhimancin amfani da kasafin kudaden kasa ta hanyar da ta dace.
Saurari wannan rahoton cikin sauti.
Facebook Forum