Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Najeriya Ta Fara Rabon Buhu 21, 924 Na Shinkafa A Katsina


Shinkafa
Shinkafa

Yayin da yake kaddamar da shirin a dandalin jama’a dake Katsina a jiya Lahadi, gwamnan ya bayyana cewa manufar shirin ita ce rage wa al’umma radadin kuncin rayuwar da suke fama da ita.

Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya kaddamar da rabon buhuna 21, 924 na shinkafa, a matsayin wani bangare shirin gwamnatin tarayya na wadata kasa da abinci.

Yayin da yake kaddamar da shirin a dandalin jama’a dake Katsina a jiya Lahadi, gwamnan ya bayyana cewar manufar shirin ita ce ragewa al’umma radadin kunchin rayuwar da suke fama da ita.

A cewarsa, shirin na nufin kaiwa ga bangarorin al’umma da dama musamman raunanan mata da kungiyoyin matasa da matakai daban-daban a mazabu da kananan hukumomi inda za’a karade jumlar rumfunan zabe 6, 652.

Ya kuma ankarar da cewar wannan shine karo na 2, da gwamnatin tarayya ke rabon kayan tallafi a jihar Katsina bayan da shugaban kasa ya samar da takin zamani ga manoman jihar domin yin amfani da shi a noman rani da damina.

Gwamna Radda ya kuma bayyana cewar a daminar bana a samu raguwar matsalar tsaro a jihar Katsina sabanin bara, domin an samu nasarar noma kaso 95 cikin 100 na gonakin jihar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG