Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kyandar Biri: NCDC Ta Tabbatar Da Samun Sabbin Mutum 8 Da Suka Kamu Da Cutar


A passenger walks past a banner informing about Monkeypox (MPOX) at Soekarno-Hatta International Airport in Tangerang on August 26, 2024.
A passenger walks past a banner informing about Monkeypox (MPOX) at Soekarno-Hatta International Airport in Tangerang on August 26, 2024.

an tabbatar da samun mutum 67 da suka kamu da cutar a jihohi 23 da Abuja daga cikin mutane 1, 031 da ake zargi sun kamu da ita da suka fito daga jihohi 35 da birnin tarayyar.

Cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta tabbatar da samun sabbin mutane 8 da suka kamu da cutar kyandar biri a kasar, inda aka samu bullarta a jihohin Gombe da Filato da Akwa Ibom.

Izuwa yanzu, an tabbatar da samun mutum 67 da suka kamu da cutar a jihohi 23 da Abuja daga cikin mutane 1, 031 da ake zargi sun kamu da ita da suka fito daga jihohi 35 da birnin tarayyar.

An bayyana haka ne yayin wata ganawa da manema labarai da babban daraktan ncdc, Jide Idris, ya kira.

Game da cutar kwalara kuma, ncdc tace ta samu mutane 141 da ake zargin sun kamu da ita da kuma mutum guda daya mutu, inda kididdigar yawan wadanda cutar ta hallaka a jihohin Katsina da Legas da Kano da Jigawa da Adamawa ta kama kaso 0.7 cikin 100.

Izuwa yanzu, an samu mace-mace 216 daga jumlar mutane 7, 663 da ake zargin sun kamu da cutar a fadin Najeriya.

Duk da cewar shugaban hukumar ta NCDC ya tabbatar da raguwar adadin wadanda suka kamu da cutar kwalara, ya bayyana cewar za’a samu karuwar barkewarta a makonni masu zuwa saboda ambaliyar ruwan da ake samu a wasu sassa na kasar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG