Trump ya fadi hakan ne yayin da yake ganawa da Firayi Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a wurin taron kolin tattalin arziki na kasashen duniya a birnin Davos na kasar Switzerland, inda ya zargi Falasdinawa da rashin girmama Amurka, bayan da Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas yaki ganawa da mataimakin shugaban Amurka Mike Pence yayin da yake ziyara a yankin.
Trump yayi barazanan yanke taimakon da Amurka ke yiwa Falasdinawa.
Wani bangaren kudin taimakon ne zuwa kai tsaye a hannun hukumomin Falasdinawan, yayin kaso mai yawa ke zuwa ga kungiyoyi masu zaman kansu da kuma kungiyoyin bada agaji dake aiki a wurin.
Idan aka kwatanta da taimakon da Amurka ta baiwa Isira’ila, a shekarar 2016, na dala biliyon uku da miliyon dari na taimakon soji. Kudin taimakon zai karu a shekarar ta 2019.
Ba za’a iya sa farashi akan yanci da mutuncin wata al’umma ba. Jiya Alhamis jakadan Falaadinawa a Majalisar Dinkin Duniya Riyad Mansour ya yi wannan furucin a New York. Yace ba zasu girgiza da barzana ko tsoratarwa ko wata muguwar niya ba, kuma ya kamata duk wani mai son zaman lafiya da adalci kuma ya amince da dokokin kasa da kasa yayi Allah wadai da wannan abu.
Mansour yayi wadannan kalaman ne a wani zama da kwamitin sulhun MDD yayi a kan Gabas ta Tsakiya.
Facebook Forum