Shugaban Amurka Donald Trump ya musanta cewa tattaunawar da ake yi tsakanin Amurka da China da zummar warware takaddamar kasuwanci ta wargaje, kuma ya na bayyana al'amarin, wanda akasari Ake kira yakin-kasuwanci tsakanin kasashe biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya, da “dan rashin fahimtar."
"Ana kan tattaunawa. Kuma har kullum za a cigaba da yi," in ji Trump, lokacin da yake amsa tambayoyin Muryar Amurka a farfajiyar kudu ta fadar White House, a jiya Talata. Ya kara da cewa, "Saura kiris mu cimma jituwa sai kawai su ka saba."
A sakamakon haka, jami'an gwamnati sun ce Shugaban na Amurka, a wannan makon, ya yanke shawarar zurfafa abin da suka fito kiri-kiri su ka kira: yakin kasuwanci da cinikayya tsakanin Amurka da China.
"Ba wanda kan yi nasara a yakin kasuwanci da cinikayya," in ji shugaban Majalisar Dattijai Mitch McConnell, lokacin da yake ganawa da manema labarai, bayan jawabin Trump. Ya ce, "Muna fatan wadannan matakan za su sa mu cikin yanayi mai kyau."
Facebook Forum