Tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden, wanda ake ganin shi ne 'yan Demokrat zasu tsayar dan takarar shugaban kasa a zaben da za a gudanar a watan Nuwanba, ya zargi Shugaba Donald Trump, da jan kafa wajen dakile barazanar da cutar Coronavirus ta haddasa a kasar.
A cewar Joe Biden "Trump ya kasa tabuka komai wajen magance bazuwar annobar."
"Al'amari ne na gaggawa, kuma bana zaton ana yin hakan” a cewar Biden a wani shirin gidan talabijin na ABC mai suna This Week.
Ya fadi cewa Trump na bukatar yayi hanzari, ya gaggauta wajen magance bazuwar annobar.
Yayin da yake sukar Biden a baya bayan nan, a jawabinsa ga manema labarai, Trump ya yaba da yabonsa da yayi game da matsayin da ya dauka na dakatar da saukar jirage daga China, a lokacin da aka bada sanarwar barkewar cutar Coronavirus a birnin Wuhan na kasar China.
Facebook Forum