Shugaba Donald Trump, ya ce zai janye Amurka daga wata yarjejeniyar kasa da kasa da aka kulla shekaru 18 da suka wuce, wacce ta ba mambobin da suka rattaba hannu ikon sa ido kan sansanonin sojin kasashen juna, saboda a cewarsa, Rasha ba ta mutunta wannan yarjejeniyar.
Amurka dai ta fara ba mambobin wannan yarjejeniya su 33 sanarwar ficewa daga wannan matsaya da aka cimma inda ta debi wa’adin watannin shida a matsayin sanar da su matsayarta ta ficewa.
Shi dai shugaba Trump na zargin Rasha da kin bin ka’idojin wannan yarjejeniya, kamar yadda ya fadawa manema labarai a Fadar White House.
A cewarsa, Amurka na da “kyakkyawar dangantaka da Rasha. Amma kuma Rashan ba ta bin ka’idojin wannan yarjejeniya, saboda haka Amurka za ta fice har sai Rasha ta shiga taitayinta.”
Ita dai wannan yarjejeniya, ta ba kasashen 35 da suka rattaba hannu akanta, damar yin leken asiri ta hanyar amfani da jirgin sama kan sansanonin dakarun mambobin kasashe da zummar tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a tsakanin kasa da kasa
Sai dai Amurka ta zargi hukumomin Moscow da take wannan matsaya da aka cimma inda takan hana wani jirgi ya yi shawagi a yankin birnin Kaliningrad da ke yankin Tekun Baltic a kusa da kan iyakar kasar ta Rasha da kasar Georgia, wadanda duk sun rattaba hannun akan yarjejeniyar.
Amma hukumomin Rasha sun musanta duk zargin da ake musu kan take yarjejeniyar.
Facebook Forum