Tun a jiya Alhamis aka fara bikin rantsar da sabon shugaban Amurka, Donald Trump, a birnin Washington DC. Zababben shugaban ziyarci wani bukin ajiye furanni da akayi a makabarta ta 'kasa a jiya alhamis, daga nan ne aka fara bikin rawa a dandalin Lincoln Memorial. ya kuma kammala da wata liyafa da aka shiryawa mutanen da suka taimaka lokacin zabe.
Hotuna: Shirye-shiryen Bikin Rantsar Da Sabon Shugaban Kasar Amurka

1
Tuta dauke da hotan zababben shugaban Amurka gabannin bukin rantsarwa a Washington DC.

2
Donald Trump a lokacin bukin ajiye furanni a makabartar 'kasa.

3
Dubban mutane na kallon shugaban Donald Trump yana ajiye furanni a makarbarta.

4
Sojojin Amurka na maci a bukin ajiye furanni a makabartar 'kasa.