A siyasar Amurka kuma, jihohi biyar ne suka yi zaben fidda 'yan takara ranar Asabar, domin tantance wadanda zasu yi takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyun Democrat da kuma Republican.
Jam'iyyar Republican ta gudanar da zabubbuka a jihohi hudu, inda mutumin da yake kan gaba tsakanin masu takara a jam'iyyar, Donald Trump, ya sami nasara a jihohi biyu- Lousina, da kuma Kentucky, shi kuma senata Ted Cruz, ya lashe zaben da aka yi a jihohin Maine da kansas. Sannan senata Marco Rubio, da kuma gwamna John Kasich na jihar Ohio, suke baya, a zabubbukan da aka yi a duka jihohin hudu.
A zaben na jiya, senata Cruz, ya sami wakilai watau delegates, fiyeda Donald Trump, duk da haka har yanzu Trump ne yake kan gaba da wakilai 378, yayinda Cruz yake da wakilai 295.
A bangaren 'yan jam'iyyar Democrat kuma, Senata Bernie Sanders, ne ya lashe 'yar tinken da aka yi a jihohin kansas da Nebraska, ita kuma tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, ta sami gagarumar nasara a zaben da aka yi ajihar Louisiana.
A gaskiya ma Clinton ta sami wakilai fiyeda senata sanders, kuma tana can gaba da shi sosai a yawan wakilai.
Madam Clinton ahalin yanzu dai tana da wakilai 1,121, idan aka kwatanta da Senata Sanders wanda yake da wakilai 479.