Da yake bayyana sabuwar dabararsa ta tsaron kasa a cikin wani jawabi daga gabatar a birnin Washington, Trump ya bayyana Rasha da China a matsayin babban damuwarsa, yana cewar kasashen biyu suna kalubalantar darajar Amurka da tasirinta da kuma arzikinta.
Amma ya yi alkawari Washington karekashin jagorancin shi ba zata ja da baya ba.
Trump yace sabuwar dabarar tsaron kasar da ya baiyana matsayin sake komawa ga hikimar iyayen kasa, zata zama tafarki ko kuma taswirar ci gaban Amurka.
A halin da ake ciki kuma, gwamnatin shugaba Trump ta yi amfani da karfinta na hawan kukerar naki a MDD a jiya Litinin ta tare kudurin kwamitin sulhu na MDD da ya yi watsi da shawarar Amurka na daukar birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila da kuma mayar da ofishin jakadancinta a wurin.
Babu wata kasa da zata fadawa Amurka inda zata kai ofishin jakadancinta, inji jakadiyar Amurka a MDD Nikki Haley.
Facebook Forum