Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Zai Halarci Taron Shugabannin Kungiyar G-20 A Brazil


Shugaban na Najeriya zai halarci taron ne a bisa gayyatar takwaransa na Brazil kuma shugaban kungiyar G-20 mai ci, Luiz Inacio Lula da Silva.

A yau Lahadi Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai bar Abuja zuwa birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil, domin halartar karo na 19 na taron kolin shugabannin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a duniya da ake yiwa lakabi da G-20, a kasar dake nahiyar Amurka ta Kudu.

Taron wanda zai gudana tsakanin Litinin 18 da Talata 19 ga watan Nuwanbar da muke ciki, zai tattaro shugabanni daga kasashe 20 mafi karfin tattalin arziki a duniya, ciki har da tarayyar Turai da takwararta ta nahiyar Afrika da hukumomin hada-hadar kudi na kasa da kasa.

Taron na bana, mai taken, "gina duniya mai cike da adalci da dorewar al'amura." zai kai mahalartansa ga tattauna batutuwan da suka shafi yaki da yunwa da talauci, da yin gyara a tsarin shugabancin duniya da cigaba mai dorewa da kuma sauya makamashin da ake amfani da shi.

Najeriya ta jima tana neman ayi garanbawul ga tsarin hukumomin dake jagorancin duniya kuma sau da dama tana gabatar da cancantarta a matsayin mai takarar kujerar dindindin a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

Kuma ana sa ran Shugaba Tinubu ya gudanar da tarurrukan kasa da kasa a gefen taron na G-20 da nufin bunkasa sauye-sauyen tattalin arzikin Najeriya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG