Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Rantsar Da Ministocinsa


Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da ministoci 45 a ranar Litinin, bayan kusan watanni uku da rantsar da shi a matsayin shugaban kasa.

WASHINGTON, D.C. - A ranar 29 ga watan Mayu, Tinubu mai shekaru 71 ya karbi ragamar mulkin Najeriya bayan lashe zaben da aka yi a bana.

Tinubu ya nada tsohon ma’aikacin bankin zuba jari Olawale Edun a matsayin ministan kudi da kuma kula da tsare-tsare kan harkokin tattalin arziki.

Ya kuma nada Heineken Lokpobiri a matsayin karamin ministan man fetur da Ekperipe Ekpo a matsayin karamin ministan albarkatun iskar gas.

Amma har yanzu ba a nada babban ministan man fetur na kasa ba, abin da ake ganin ya yi kamanceceniya da abin da tsohon Shugaba Muhammad Buhari da ya gada ya yi.

Idan za a iya tunawa Shugaban Tinubu ya kai wa Majalisar Dokoki sunayen wadanda yake so a tantance kusan makonni uku da suka wuce.

A lokacin tantancewar Majalisa ba ta sahale sunayen mutum uku ba, ciki har da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El’Rufai.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG