Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Rantsar Da Kekere-Ekun A Matsayin Alkalin Alkalan Najeriya


Mai Shari’a Kekere-Ekun, Alkalin Alkalan Najeriya Ta 23
Mai Shari’a Kekere-Ekun, Alkalin Alkalan Najeriya Ta 23

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya rantsar da Kudirat Kekere-Ekun a matsayin babbar jojin Najeriya.

Bikin rantsarwar ya gudana ne a babban dakin taro na fadar shugaban kasar dake Abuja.

Rantsar da Kekere-Ekun a matsayin cikakkiyar alkalin alkalan najeriya ya biyo bayan tabbatar da ita da Majalisar Dattawa tayi a makon da ya gabata.

A Agustan da ya gabata, Majalisar Harkokin Shari’a ta kasa (NJC) ta baiwa Shugaba Tinubu shawarar nada Mai Shari’a Kekere-Ekun a matsayin wacce zata gaji tsohon babban jojin Najeriya, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola.

Kekere-Ekun ce babbar jojin Najeriya ta 23 kuma mace ta 2 da ta taba hauwa wannan mukami.

Mace ta farko da ta hau kan wannan mataki ita ce Mai Shari’a Maryan Aloma Mukhtar, wacce ta rike mukamain alkalin alkalan Najeriya tsakanin watan Yulin 2012 da Nuwambar 2014.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG