Babbar Mai Shari’a a Najeriya (CJN) Kudirat Kekere-Ekun, ta ce ba za ta lamunci cin hanci da rashawa ba a karkashin shugabancinta.
Kekere-Ekun ta bayyana hakan ne a ranar Laraba bayan da majalisar dattawa ta tabbatar da ita a matsayin sabuwar Babbar Mai Shari’a a kasar.
Hakan na nufin ita ce mace ta biyu da ta taba rike wannan mukami a Najeriya.
“Dukkan kararrakin da aka shigar wadanda suka shafi batutuwan da suka faru gabanin zabe, za a kammalu su a kotun daukaka kara.” Kekereke-Ekun ta ce.
‘Yan majalisar Dattawan sun kwashe sa’o’i suna ta mata tambayoyin kan shirinta na samar da sauye-sauye a fannin shari’ar kasar.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya aika wa majalisar dattawa bukatar a tantance Kekereke-Ekun.
A watan Agusta Tinubu ya ba ta rikon kwarya sakamakon ritayar Mai Shari’a Olukayode Ariwoola da ya gabace ta.
Dandalin Mu Tattauna