Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Nemi A Warware Sabanin Da Ke Tsakanin Kamfanin Jiragen Sama Na Emirates Da Najeriya


Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya ba da umarnin cewa a gaggauta warware sabanin da ke tsakanin Najeriya da kamfanin jiragen sama na Emirates EMIRA.UL da kuma bayar da bizar zuwa hadaddiyar daular Larabawa, in ji kakakin shugaban kasar a ranar Alhamis.

WASHINGTON, D.C. - Daular Larabawa ta dakatar da bayar da biza ga 'yan Najeriya ne a shekarar da ta gabata, bayan da kamfanin jirage na Emirates ya dakatar da zirga-zirgarsa zuwa kasar saboda gazawar samun kudadensu da suka makale a Najeriyar wacce ta fi kowace kasa girman tattalin arziki a nahiyar Afirka.

Jirgin saman Emirates
Jirgin saman Emirates

A wata sanarwa da ofishin Tinubu ya fitar a ranar Alhamis ya ce ya gana da jakadan UAE a Najeriya, Salem Saeed Al-Shamsi, inda ya kara da cewa a shirye yake "da kansa" ya shiga cikin sabanin domin samun daidaito.

"Dole ne mu yi aiki tare. Muna bukatar amincewa da muhimman batutuwan da suka shafi jiragen sama da na shige da fice," in ji Tinubu a cikin sanarwar.

Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Sanarwar ta ruwaito Al-Shamsi yana cewa, "muna hanyar samun mafita. Waɗannan kananan batutuwa ne, mu, kamar iyali daya ne, kuma za a warware su."

Kamfanin jiragen sama na Emirates ya ce a watan Maris da ya gabata yana da “dumbun kudaden shiga” da suka makale a Najeriya kuma yunkurin karbo su na tafiyar hawainiya.

Najeriya ta na rike da akalla dala miliyan 743 na kudaden shiga da kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa da ke aiki a kasar suka samu, kungiyar kamfanonin jiragen sama ta duniya IATA ta fada a watan Maris.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG