Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Kafa Tarihi Wurin Aika Wa Majalisar Dattawa Sunayen Ministoci 48


Majalisar Dattawan Najeriya
Majalisar Dattawan Najeriya

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa tarihi a daidai lokacin da ya aika wa Majalisar Dattawa sunayen mutane 48 domin a tantance su a matsayin ministoci.

Wani abu da ya dauki hankali shi ne akwai dan asalin Birnin Tarayya a jerin sunayen. Wannan ma abu ne da ba a taba yi ba, to sai dai masana tattalin arziki na cewa za a samu matsala domin a yanzu ma bashi ake karba a biya albashi.

Wani abin dubawa a wannan shi ne cewa babu gwamnatin da ta taba nada ministoci masu yawa a kasar tun bayan dawowar mulkin dimokradiyya.

Idan an bi tarihi, a wannan jamhuriya ta hudu da ta fara a shekara 1999, an samu Shugaba Olusegun Obasanjo ya nada ministoci 27 tsakanin mulkin sa na farko daga 1999 zuwa 2003, wanda ya kai adadin su zuwa 30 a wa'adinsa na biyu daga shekara 2003 zuwa 2007.

Olusegun Obasanjo
Olusegun Obasanjo

A shekara 2007 zuwa 2010 marigayi Umaru Musa Yar'aduwa ya kai adadin 39, amma bayan rasuwar sa sai Shugaba Goodluck Jonathan ya rage yawan su zuwa 33.

Kundin tsarin mulki ya tanadi cewa za a nada Ministoci 36 ne, idan an hada da babban birnin taraiyya kuma, sai a nada 37.

Sen Rufa'i Sani Hanga ya ce Majalisa za ta yi zama na musamman akan ministocin, domin tantance su ba shi ne yake nufin Majalisar dattawa za ta amince da duka jerin sunayen ministoci 48 da shugaba Tinubu ya aika da su ba. Hanga ya ce ya ja hankalin shugaban kasa kan yawan ministocin da ya bayar 48 inda ya ce sun yi yawa duba da yanayin da kasar ta ke ciki na matsin tattalin arziki da kuma irin makudan kudaden da za a rinka kashewa akan su.

Amma ga shugaban Kungiyar ceto APC (RESCUE APC NORTH WEST GROUP) Muktar Dahiru Gora, ya ce kungiyar tana murna da yadda jamiyyar APC ta samu gata, inda ya ce Shugaban Majalisa na Arewa Maso Yamma, haka Mataimakin Shugaban Majalisar dattawa, da Kakakin Majalisar Wakilai sannan kuma ga Ministoci da dama daga shiyyar Arewa maso yamma.

Amma Dahiru ya ce sauya sunan Maryam Shetty bai yi wa kungiyar dadi ba, duk da cewa Mulki na Allah ne, yana iya baiwa wanda ya so, kuma ya hana wanda ya so. Sai dai yana fata za a ba ta wani mukami nan gaba. Dahiru ya ce kungiyar tana murna tun da an sake ba wata mace daga Kano kujerar Ministar.

To sai dai kwararre a fannin tattalin arziki na kasa da kasa Shuaibu Idris Mikati ya koka ne kan yadda aka samu ministoci har 48.

Mikati ya ce tsarin mulki ya bashi dama ya nada ministoci 36 ne, saboda haka masana kimiyan Mulki suna tsananin mamakin yawan ministoci da ya ke neman ya nada, saboda ba a taba yi ba a tarihin kasar nan. Mikati ya ce kasar tana fama da dimbin bashi, ga talauci ya yi wa mutane katutu, ga kuma wahalar da cire tallafin man fetur ya ja wa al'umman kasa. Mikati yana mai bada shawarar a sake dubawa da idon basira.

Bincike da Muryar Amurka ta yi na nuni da cewa idan aka nada ministoci 48 din nan, kasa za ta iya kashe Naira biliyan 3.3 kan ministocin a cikin shekara hudu.

Saurari rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG