Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Kaddamar Da Sabuwar Tashar Wutar  Lantarki A Abuja


Malam Mele Kyari Suhugaban NNPC, Najeriya
Malam Mele Kyari Suhugaban NNPC, Najeriya

Ana sa ran wannan aiki zai samar da Megawatt 350 cikin 1, 350, wanda ya kasance kashi na farko na baki dayan aikin.

ABUJA, NIGERIA - A daidai lokacin da ake kwan gaba-kwan baya a game da matsaloli masu alaka da wutar lantarki a Najeriya, Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar da aikin gina tashar samar da wutar lantarki mai zaman kanta a yankin Gwagwalada na birnin tarayyar Abuja.

Aikin da kamfanin kasuwancin man kasar na NNPCL tare da hadin gwiwar wasu kamfanonin makamashi na kasashen waje ne suka kulla don biyan bukatar samar da karin iskar gas da zai taimaka wajen bunkasa harkar samar da wutar lantarki a kasar.

Babban Sakataren FCTA
Babban Sakataren FCTA

A lokacin kaddamar da gagarumin aikin na wutar lantarkin, Shugaba Bola Tinubu ya nuna farin cikinsa, yayin da yake yi wa ‘yan Najeriya jawabi a bikin kaddamar da daya daga cikin muhimman aikin samar da ababen more rayuwa na kasa.

Ana sa ran wannan aiki zai samar da Megawatt 350 cikin 1, 350, wanda ya kasance kashi na farko na aikin gaba daya wanda ake matukar bukata.

Sabuwar Tashar Wutar Lantarki A Gwagwalada, Abuja
Sabuwar Tashar Wutar Lantarki A Gwagwalada, Abuja

A cewar Shugaba Tinubu, wannan matakin da aka dauka na da matukar muhimmanci ga al'ummar kasar domin ya zama mataki na farko da za a dauka a kokarin da gwamnatinsa ke yi na kafa wani bangare mai karfi sosai wanda zai tafiyar da tattalin arzikin kasar.

A cewar Tinubu, makamashi shi ne mafi muhimmancin abin da ‘dan adam ya gano a cikin shekaru dubu daya da suka gabata, yana mai cewa ba za’a yi rayuwa mai inganci ba, ba wutar lantarki, kuma Najeriya na buƙatar makamashi ainun.

Mahalartan Gudanar Da Tashar Wutar Lantarki A Gwagwalada, Abuja
Mahalartan Gudanar Da Tashar Wutar Lantarki A Gwagwalada, Abuja

Kazalika, shugaba Tinubu ya ce, a lokacin yakin neman zabensa, ya yi wa ‘yan Najeriya alkawarin tabbatar da bai wa aikin samar da wutar lantarki fifiko a karkashin Gwamnatinsa.

Wani Basarake a Gwagwalada, Abuja
Wani Basarake a Gwagwalada, Abuja

Shugaban kamfanin man fetur na kasar wato NNPCL, Malam Mele Kolo Kyari, ya ce kasancewar ana fama da karancin wutar lantarki wanda ba ya yin daidai da bukatar ‘yan kasa saboda wasu ayyukan da ya kamata a yi su da dadewa amma ba’a sami aiwatarwa ba, yanzu an sami dama kuma wannan aikin zai taimaka wajen samarwa kamfanonin damar yin aiki yadda ya kamata kuma ‘yan kasa ma za su sami guraben ayyukan yi.

Mahalarta A Lokacin Bude Tashar Wutar Lantarki A Gwagwalada, Abuja
Mahalarta A Lokacin Bude Tashar Wutar Lantarki A Gwagwalada, Abuja

Kamfanin kasuwancin man fetur na Najeriya NNPCP tare da hadin gwiwar kamfanin makamashin General Electric, da kamfanin samar da kayayyakin aikin injiniya mallakin kasar Sin wato CMEC ne ke aiwatar da aikin samar da tashar wutar lantarkin mai megawatt 350 cikin dubu daya da 350 a nan Abuja.

Saurari cikakken rahoto daga Halima Abdulrauf:

Tinubu Ya Kaddamar Da Sabuwar Tashar Wutar  Lantarki A Abuja. mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG