Suna masu gargadin Tinubu da ya dora daga inda magabatansa suka tsaya game da huldar Najeriya da kasashe makwabta.
A nasu gefe ‘yan hamayya sun yaba wa tsohon shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari dangane da yadda ya sakar wa magajinsa ragama ba tare da nuna alamun yi masa shishigi ba.
Sakarwa jama’a hanyoyin shigi da fici a tsakanin Najeriya da kasashen makwabta na daga cikin matakan da ‘yan siyasar Nijer ke fatan ganin Bola Ahmed Tinubu ya bai wa fifiko domin karfafa dadaddiyar dangantakar al’ummar kasarsa da takwarorinsu na kasashen dake kewaye da ita.
Mashawarcin shugaban kasar Nijer na musamman a fannin sadarwa Alhaji Doudou Mahamadou da aka fi sani da Doudou Rahama na ganin yin hakan a matsayin wani matakin nasarar wa’adin mulkin Tinubu na farko.
Jigo a jam’iyar Moden Lumana ta ‘yan adawa Mahamadou Maidouka na da irin wannan ra’ayi a bisa la’akari da alakar ku da kut din dake tsakanin Nijer da Najeriya.
Dagewa kan maganar inganta rayuwar ‘yan Najeriya wani abu ne da ya kamata sabon shugaban ya saka a kan gaban jerin aiyukan da yake da niyyar aiwatarwa domin samun walwalar jama’a a Najeriya abu ne da tasirinsa ka iya bayyana a kasashe makwabta.
Shugaba Muhammadu Buhari wanda a take ya koma garinsa na asali jim kadan bayan damka ragamar mulki wa magajinsa ya cancanci yabo a cewar ‘yan hamayya saboda yin hakan hujja ce da ke kara jaddada wa duniya cewa cikeken dan dimokradiya ne.
A shekarar 2015 shugaba Muhammadu Buhari bayan ya karbi madahun ikon Najeriya ya fara ziyararsa ta farko a ketare da jamhuriyar Nijer haka shi ma shugaba Mohamed Bazoum a shekarar 2021 da Najeriya ya fara rangadinsa na kasar waje abinda ya sa a yanzu haka wasu bayanai ke cewa Bola Ahmed Tinubu na da niyyar maimaita wannan al’ada ta shugabanin kasashen biyu.
Saurari rahoton Sule Barma: