Dangartaka ta kud da kud tsakanin Tillerson da shugaban Rasha Vladimir Putin, yasa Mccain da wasu senatoci sun nuna taraddadi. MCcain, wanda ya bayyana goyon bayansa a cikin wani shirin tashar talabijin ta ABC, yace wannan shawara bata zo masa da sauki ba.
Duk da goyon bayan da McCain da Graham suka bayyana, babu daya daga cikinsu dake kwamitin kula da harkokin kasashen waje, inda ake sa ran kwamitin zai kada kuri'a kan haka a maraicen yau. Senata Marco Rubio na Florida yana kwamitin kuma har yanzu bai bayyana matsayarsa ba.
'Yan Republican suna da rinjaye da senata daya a kwamitin, idan Rubio ya hada kai da 'yan Democrat suna iya kin amincewa da zaben Rex Tillerson daga kwamitin.